Google69490f6862051cb8
google-site-verification: google69490f6862051cb8.htmlgoogle-site-verification: google69490f6862051cb8.htmlgoogle-site-verification: google69490f6862051cb8.htmlBasheer journalist sharfadi14

Basheer journalist sharfadi14.jpg6
Basheer journalist sharfadi 11 1
Maraba Da Zuwa Wannan
Shafi Mai Al-barka 1

☀ Zabi inda kake son shiga ☀
Menunks
→Home
→Akidojin Ahlussunnah
→Addinin musulunci (35)
→40 Hadith (50)
→Fadakarwa (120)
→Neman labarai (20)
→Shi'a Kafirci (50)
→Hadith (55)
→Khudubobi (24)
→Tarihin magabata (60)
→Raddi / Maida martani (99)
→Face book post (30)
→Monthly Archives (60)
→Tambaya da Amsa (20)
→Sahabban Annabi {s.aw} (50)
→Taskar maluman sunnah (25)
→Akidar Y'an Shi'a Dangane da Al'kur'ani
→Fassarar Usulussunnah (20)
→Sheik Ja'afar {Rahimahullah} (65)
→Sheik Abubakar Gumi {Rahimahullah} (30)
→Sheik Dr. Muhammad Sani R/Lemo
→Salafiyyah Network Nigeria (100)
→Adam Sani Abu-Umayrah (99)
→Salaf Ustaz (79)
→Malama Ummi Ahmad Katsina
→Malama Amina Saleh Mande
→Labarai (40)
→Nishadantarwa (10)
→Siyasar Nigeria (9)
→Vidio (33)
→Audio (66)
→Hotuna (120)
→Internet Cheat (90)
→Site Achieve
→Application (10)
→Games (8)
→About me (01)

Wannan shafin mallakarCoollogo com-1281358 3
Ne




SHAFI DON KARUWAR MUSULMI
**DUNIYAR MUTUWA**(1) (Adam Sani Abu-Umayrah)

A daya daga cikin tadfiye tafiye na zuwa Birnin Riyaad, nai shirin zuwa filin jirgin sama kafin lokacin tashin Jirgin da Awa 1, sai dai cunkoson hanyar, da kuma Bincike yasa na makara a tafiyata, sai na dinga sauri har na isa wajen tsayuwar motoci, sai na dauki Kaati na (Visa) da sauri, nai Parking motata a wurinda ni bansan shin wurin Parking din ma'aikata ne ko na matafiya, ni dai na sauko da sauri daga mota na dauki Jakaata a hannuna, na shiga abin tafiya (Escalator) na isa dakin bincike, na cire duk abindake aljihuna na riqe a hannu, na danna na'urar bude qofa, amma sai naji sanarwar cewa wai a jikina akwai wani abu da bazan iya wucewa dashi ba, sai na shiga damuwa, chan sai na tuna Agogona ne ai, sai na cire, na sake danna na'urar, sai ta bude na wuce lafiya.
Na isa wajen mai bada Tikitin Jirgi da sauri, nace: Ni matafiyi ne zuwa Riyaad, cikin jirgi mai lamba 1411, sai ma'aikacin yace: Ai Jirgin ya cika, sai nace dashi: Don Allah ka taimakamin, inada Alqawarine wanda ba makawa in halarceshi a wannan Dare.
Sai yace: Kada ka yawaita magana, don Jirgi ya riga ya cika, kuma babu wanda zai daga maka qafa, sai nace: Hasbiyallah!!!!

Na fito daga wajensa, na tsaya ina kallon jirgin banida tsimi banida dabaarah face ga Allah, sai tunani yadinga ketomin akaina cikin sauri! Shin zan bar tafiyar nan ne? Kodai in tafi a Motata? Ko in dauki hayar mota in tafi? Sai dai zuciyata ta bani in tafi a motar haya, sai na koma bangaren yan Tasi (Taxi), sai na samu wani mutum cikin sabuwar Mota (Camry), na ce dashi: Nawa zaka kaini Riyaad? Yace: Riyal 500! Nayi qoqarin samun ragi wajensa, amma bai ragen komaiba illa Riyal 50.
Na hau Motar ni kadai, nace dashi yayi sauri, domin dolene na Isa Riyaad cikin wannan Dare, ni ban sani ba, ashe qarshena cikin Awanni ne!!!!!!!!
Yace dani: Sha Kuruminka, zanyi gudu dakai tamkar Tsuntsu, ai kuwa haka akai, ya dinga gudu na hauka, don na masa Alqawarin idan ya isa Riyaad dani kafin Isha'I, zan bashi qarin kyautar Riyal 100 (bayaga 450 dinsa).
Muna tafe muna hira yana tambayata ina tambayarsa muna raha, don dai mu debe kewar juna!
Kwatsam sai mahaifiyata ta fadomin qwaqwalwata akan in kiraata, ai kuwa na kirata, tace: Ina kake ne ya Aba-Saarah?
Sai na bata Labarin Jirgi, da yanda na rasa tafiya ta Jirgi, sannan yanzu na hau mota ne don tafiyar, sai tayyi shiru, wanda hakan ya janyo hankali na, sai mhaifiyata tace: Ka kula ya kai Daana, Allah kareka daga sharrin abindake boye, sai nace: Amin, zan kiraaki da zaarar na isa Inshaa Allah, kinada wasiyya gareni ne? Tace: kasancewarka Lafiya ya Tsayin Rayuwata!!!!!!......­..
Anan muka kammala waya da ita!
Sai naji wani abu a raina, nakejin wani abin Al-ajabi na shirin Aukuwa dani! Sai na kira Mataata, tace: Bani Labarinka ya rayuwata, Kilomita nawa kukai? Nace: Yanzu munyi Kilomita 150. Tace: Wallahi munyi rashinka, in baka gidannan duk babu dadi! Nace: Allah ya maki Albarka, in Allah yaso inanan dawowa a jirgin Raana, ki kula da yaara na, ki sumbancemin Susu, Allah ya kula mana da ita! Tace: albishirinka, ai tun randa ta dawo take ina Baba? Nace: Bani ita! Susu tace: Baba ina kake? Nace: Susu nan bada jimawa ba zan dawo maku inshaa Allah, muka danyi dariya nace to ba Mama wayar, sai ta bata, nace: kinada wata wasiyyace gareni? Tace: Fataana shine kubutar rayuwarka! Ban sani ba menene dalilinda yasa damuwa ta soma tsananta agreni! Na shiga Zurfin tunani wanda ban dawo ba sai ji nayi Direba na Tambayata...........­..........


Ko me Direban ya Tambayeshi? Shin ya zasu qarke a hanya, yana isa Riyaad kuwa????
Mu hadu gobe da yardar Allah.


**DUNIYAR MUTUWA**

(02)

(Ci gaba)

Bayan gama wayata da mataata, tunani ya tarun-min a raina, damuwata ta dinga qaruwa, na shiga zurfin tunani, ban Farka ba sai ji nayi Direba na Tambayata: Wai shin Yaranka nawa ne? Nace: 4, 2 maza 2 mata. Yace: Allah ya shiryar maka dasu! Nace: Amin, kaima haka.
Na kalli hanya, sannan na kalli sama ina kallonta, na kalli rana, sai naga kadan ya rage ta faadi, na fadi ina mai qura kallo: Ya Allah, Rahmarka nake kwadayi yaa Rahmaan yaa Raheem! Ban Aune ba naji direba na neman izinina wai yanaso ya kunna sigaari, sai nace: Ya kai dan'uwana, kai mutum ne me daraja, kuma ina tsammanin tattare dakai akwai Alkhairi mai girma, ya zaka yardarwa kanka ka qona kanka? Ka qona kudinka? Kuma ka tauye Addininka a dalilin Sigaari? Kuma a qarshe bata amfaanarka sai dai cutar dakai???
Sai yace: Yaa kai dan Halal, kamin Addu'a, wallahi nayi qoqarin barin shanta cikin Ramadan da ya gabata amma na kasa.
Sai nace dashi: kai mutum ne da Allah ya bashi iko amma ka kasa akan sigari??!! Naci gaba da masa nasiha da shiryar dashi, shi kuwa yana saurarena, yana mai nadamar shan sigaari da yakeyi, bayan kammalawata sai yace: Inshaa Allah daga yau bazan sake shan sigaari ba! Nace masa ina mai farin ciki: Allah ya Tabbatar damu akan Addini!

Kawai nidai zan iya tuna cewa: na jingina kaina jikin qofar motar ina tunani, na rasa menene yasani nake firgici,na rasa akan menene, gashi inajin damuwa mai tsanani a wannan lokaci, Kwatsam!!! Sai jin qara mai tsanani nayi, gaba daya ni da direba muka rikice, nasan cewa Taaya ce ta fashe, sai nace ya rage sauri, ka sanya alama (Signal) don sauran motoci susan mun samu matsala ne, shi kuwa ko magana baya iyawa, ya kankame sitiyaarin motar, Alamun damuwa cike da Fuskarsa, lokaci qanqani motar ta hantsila bangaren daama (tabi Wrong way) ta dinga qundun baala, nidai Allah ya taimakeni inata fadin "Laa ilaaha illallaah, Muhammadur-Rasululla­ah" inajin kamar ina daga muryata da ita ne, bayan nan naji wani duwka mai qarfi ta qasan kaina, naji tamkar harshen wutane sabida tsabagen zaafinta! Motar ta wuntsula ba adadi, hardai ta tsaya, a nan ne nayi yunqurin fitowa in miqe, amma na kaasa, na kaasa koda motsa ga6a 1 ta jikina, naji wani irin radadi wanda ban tabajinsa ba a rayuwata, na kaasa magana, idanuwana a bude suke, amma bana iya ganin komai in banda duhu!
Chan sai naji sautin takalman mutane na gabatowa kusa da mu, ina ji suna cewa: kada ku tabashi, kanshi na zuban jini qafarsa ta karye, sai na soma jin numfashi na na tsananta, naji wani irin zaafi mai tsanani na tasowa daga qafata zuwa kai na!
Sai naji suna cewa: ina direban yayi ne? Sai naji wani mutum yace: kuji sautinsa chan nesa, yana neman taimakonku, mutuwa zai ba makawa baya iya motsi!!!!!!!
Naji Radadin na qaruwan min, inata tunane-tunane! Shin wannan ne qarshena? Subhaanallaah! Na soma nadaama mai tsanani bisa lokutan da na baata a rayuwata, da taqaita ayyukan Alheri da na dingayi a rayuwata! Yanzu gaani a lamarinda dole mai aukuwa ne ba makawa! Sai na soma jin sautin mutane na bace min, duhu ya soma tsananta a idona, radadi kuwa tamkar ana yayyanka jikina da wuqaqe, sai naji kamar wani abu na maaqureni, yana hana iska zuwa min! Anan na tabbata rayuwata ta yanke kenan!
Chan sai ga wani mutum ya zomin, cikin tsananin duhu da nake gani, yazo min da Gemuna fari Fat!!!!!!!


Ku biyoni gobe da Yardar Allah don jin wanene wannan Mutumi? Me yazowa wannan Baawan Allah dashi bayan Mutuwarsa? Mai zai faru da wannan Mutumi bayan Mutuwarsa?

**Dan uwa shin kana shirin mutuwa, kokuwa kana tsammanin ta tsoffi ce?????**


**DUNIYAR MUTUWA**

(3)
CI GABA................­.


Chan sai ga wani mutum ya zomin, cikin tsananin duhu da nake gani, yazo min da Gemuna fari Fat, Ya ce dani: Yaa kai Daana, wannan itace qarshen rayuwarka, kuma nazo maka ne ina mai maka nasiha kafin ka hadu da Uban-gijinka, Haqiqa na sanka, kai mutum ne mai hazaaqa, kana son Alkhairi, don haka da sannu zan maka wasiyya da wata wasiyya, domin Allah ne ya aikoni wajenka.
Sai nace: Menene kake so?
Sai yace: Kace: "Na yi Imaani da Cross", domin na rantse da Allah shine kubutarka, idan kai Imaani dashi zan maisheeka ga iyaalanka da yaaranka, sannan in mayas maka da ranka, ka fadi haka da sauri, bamuda lokacin tsaiko!.
Na san wannan shine Shaidan, dukda irin radadinda nake fama dashi na fitar raina, ban gushe da Yarda ga Ubangijina ba da Annabina s.a.w.
Nace masa: Maza juya kabani waje ya maqiyin Allah, haqiqa na rayuwa musulmi, kuma da izinin Allah zan mutu akan haka.
Sai Fuskarsa ta chanza yace: Ka saurareni, bazaka kubuta ba a yanzu, face ka mutu banasare ko bayahude, in kuwa kaqi, zan qaara maka radadi kuma in dauki ranka.
Nace: Rayuwa da Mutuwa duk suna hannun Allah ne, ba a hannunka ba, ni bazan mutuba sai akan Musulunci, sai fuskarsa ta yamutse, shaidaanin yace: idan ka fitineni (kaqi bin umarnina) to Daruruwanka bazasu iya ba! Kuma ya isheni tunda na iya sanyaka kana saabawa Allah da yawa, kuma kana keta iyakokinsa.
Sai naga ya kalli sama, kamar ya hango wani abu da yake tsoro, sai ya gudu da sauri, sai nai mamakin saurin wucewarsa, kuma nai mamakin menene abinda ya tsoratashi haka! Ban dauki wani lokaciba, sai naga wasu fuskoki baaqi agreni masu girman Halittaar jiki sun sauko a gareni, suka ce min: Assalaamu Alaikum.
Nace: Wa'alaikumus-Salaam.
Sai sukai Shiru basu ce komai ba, taredasu akwai Likafani, sai nasan wannan itace qarshe ba makawa, sai wani malaa'ika mai matuqar Girma ya sauko, yace: "Yaa ke rai natsatstsiya, ki fito zuwa ga gaafara daga Allah da Yarda....
Wallahi sai naji Amince wanda bazan iya misaltawa ba a sanda naji wannan Kalmah daga gareshi, nace masa: Bushaararka ya Malaa'ikan Allah!
Sai ya cire raina, na kasance tsakanin yanayin barci da Haqiqa, naji Tamkar ina miqewa daga jikina ina hawa sama, na waigo qasa sai naga jikina mutane sun dabai-bayeshi, sun sanya mayaafi akan jikina, inaji wasunsu na cewa: Innaa lillaahi wa innaa ilaihi raaji'un!!!!
Naga Tamkar Malaa'iku 2 sun daukeni sun sanyani cikin likafanin cikin sauri, sun daga sama dani, ina waiwayawa daama da hagu, na hango rufin sama chan nesa, ahaka suna qaara dagaawa dani, muna keta giraagizai, tamkar ina cikin jirgi, har na soma ganin mutane qananaa-qanaana a qasana, sukaci gaba da gudu dani zuwa sama, har na soma ganin qasa tamkar qwallo qarama, sai na cewa Malaa'ikun: Shin Allah zai shigar dani Aljannah? Sukace: wannan saninsa na wajen Allah, mudai Malaa'ikune da aka wakiltamu don daukan ran Musulmai kadai.
Dukanmu sai Hankalinmu ya karkata ga wasu Malaa'iku da mukaga sunzo sun wucemu da sauri, dauke da wata Ruhi mai tsananin Qamshi, inda na shaqi qamshin miskinda ban taba shaaqar tamkarsaba a rayuwata, nacewa Malaa'iku: Wanene wannan? Nidai banda nasan cewa Annabi Muhammad s.a.w shine qarshen Annabaawa, da nace wannan Ruhin Annabi ne! Sabida Rakiyar Malaa'iku da na gani sun mata, da Qamshinta gamida yanda suke riqe da ita cikin Girmamawa da Karramaawa!


Allahu Akhbar! Jama'a Kunsan Wannan Gaawar wacece? Mu hadu a kashi na 4! Sannan maji yanda wannan Bawan Allah tafiyar ruhinsa zuwa sama ta kasance, da yanda zai dawo bayan Mutuwa!


Naku: #Abu_Umayrah


**DUNIYAR MUTUWA**

(4)

Dukanmu sai Hankalinmu ya karkata ga wasu Malaa'iku da mukaga sunzo sun wucemu da sauri, dauke da wata Ruhi mai tsananin Qamshi, inda na shaqi qamshin miskinda ban taba shaaqar tamkarsaba a rayuwata, nacewa Malaa'iku: Wanene wannan? Nidai banda nasan cewa Annabi Muhammad s.a.w shine qarshen Annabaawa, da nace wannan Ruhin Annabi ne! Sabida Rakiyar Malaa'iku da na gani sun mata, da Qamshinta gamida yanda suke riqe da ita cikin Girmamawa da Karramaawa!
Sai suka ce: wannan Ruhin shahidi ne da yayi shahaada a Palastine, dazunnan Yahudawa suka kasheshi, yana mai kaariya ga Addininsa da Garinsa, Haqiqa Allah ya sa yanada yawan Ibaadah gashi Mujaahidi!
Sai nace: kaicona ma ace nayi mutuwar Shahaadah ne!
Ba'a jimaba sai naga wasu Malaa'ikun dauke da wata ruhi abar qyama, wani wari mai doyi na tashi daga gareta! Sai nace waye wannan?
Sai sukace: Wannan Mutumin Handusa ne, yana daga cikin Masu bautar shaanu, ya mutu ba da jimawa ba bisa tsawa da Allah ya turo masu, sai na gode Allah bisa ni'imar Musulunci.
Sai nace masu: wlh duk yanda na karanta wadannan abubuwa, banyi zatonsu haka ba, sai malaa'ikun sukace: Bushaararka da Alkhairi, amma ka sani Al'amarindake gabanka mai tsayi ne.
Sai nace ina mai mamaki: Yaya kenan?
Sukace: duk zaka ga haka, sai dai munaso ka kyautata zatonka ga Ubangijinka.
Muka wuce wata jamaa'ah ta mala'iku mukai masu sallama, sai sukace: waye wannan? Sai mala'ikun sukace: wani mutum ne musulmi, dazunnan yayi hatsari sai Allah ya Umarcemu da muje mu dauko ransa daga mala'ikan mutuwa, sai malaa'ikun sukace: Lallai Allah mafi ni'ima ne da Karamci ga musulmai, domin su Alheri ne kuma Alherine qarshensu!
Sai nacewa Mala'ikun nan 2: suwa wadannan? Sukace: wadannan mala'ikun sune masu gadin sama, kuma sune masu wurga shahab (taurari da ake jifan aljanu dasu) ga shaidanu!
Sai nace: Lallai halittarsu mai girma ce, sai sukace: ai akwai wadanda suka fisu girma ma! Sai nace: su waye? Sukace: Jibril da masu riqo da Al-arshi! Kuma su halittane daga halittun Allah basu saba masa bisa umarninsa kuma suna aikata abinda aka umarcesu! Nace: Tsarki ya tabbata gareka ya Allah, haqiqa bamu bauta maka ba kamar yanda ya kamata!
Sannan muka isa saman Duniya, haqiqa na kasance tsakanin shauqi da mamaki! Sabida abinda na gani, kuma tsakanin tsoro da da firgici..
Naga saman duniya mai girmace matuqa, tanada qofofi a rufe, akan kowace qofa akwai Mala'ika mai matuqar girma a tsaye, sai Malaa'ikun nan 2 sukace: Assalamu alaikum wr wb, nima nai sallamar tare dasu, sai suka amsa mana: Wa'alaikumus-salaam wr wb, sukace: maraba da Malaa'ikun rahmah, suka dubesu suka ce: ba makawa wannan Musulmi ne! Sukace: Tabbas kuwa, is Malaa'ikun (dake gadin qofofin sama) suka ce:ku shigo, domin ba'a bude qofofin sama face ga Musulmai, domin Allah na cewa: ((Lallai ne wadanda suka qaryata ga ayoyin mu, kuma suka bijire mata, ba'a bude masu qofofin sama, kuma bazasu shiga Aljannah ba har sAi raqumi ya fita ta kafar Allura, hakan ne muka sakankawa masu laifi)) A'araaf:40.
Sai muka shiga, naga abin mamaki, naga wani gini babba tamkar ka'abah, mala'iku masu yawa na dawafi akewayenta, nace: wannan lallai shine BAYTUL-MA'AMUR, mala'ikun sukai murmushi sukace eh, Alhmdlh, mafi yawan wadanda mukazo dasu nan daga Musulmai suna gane wannan wuri, wannan kuma falalar Allah ne kuma falalar Mutumin qwarai Annabinku Muhammad s.a.w wanda bai bar wani abu ba face ya sai ya sanar daku! Sai nace dasu: mala'iku nawane ke zuwa nan kullum? Sukace: Dubu 70, kuma da sun wuce basu dawowa! Sai muka daga cikin tsananin sauri zuwa sama ta biyu.




Mu hadu a kashi na 5!


**DUNIYAR MUTUWA**

(5)

Da muka isa sama ta 2, nanma aka bude mana har muka isa ta 7, sai naga itace mafi girman sammai, sai naga tamkar rafi agabanmu, naga Mala'iku sun sunkuyas da kawunansu, suka ce: "Allahumma innaka antas-salaam waminkas-salaam tabaarakta ya zhal-jalaali wal ikraam" sai naji wani firgici, na qasqantar da kaina hawaye na zubomin, sai Allah yacewa Mala'ikun: "Ku sanya littafin bawana cikin illiyin (shine rukunin da ake sanya littafan yan Aljannah -Allah ka sanya mu cikinsu-), kuma ku maisheshi zuwa qasa, domin daga gareta na haliccesu kuma cikinta zan maishesu kuma daga gareta zan tashesu wani lokaci na daban. Sabida tsananin Firgici, tsoro, da farin ciki da Murna, ban iya cewa komai ba sai: Tsarki ya tabbata gareka, bamu bauta maka ba yanda ya kamata!.
Sai mala'ikun nan suka sauko dani zuwa qasa, duk sanda muka hadu da mala'iku sai muyi masu sallama, sai nacewa Mala'ikun: shin zai yiwu nasan abinda ya faru da gangan jikina da iyalaina?
Sai sukace: jikinka dai zaka ganshi, amma iyalanka ayyukansune kawai da zasu dinga maka kyautarsu zasu dinga riskarka, amma bazaka gansu ba! Suka dawo dani qasa, suka ajeni kusa da jiki na, sukace: ka kasance a jikinka, mu aikinmu ya qare anan, bayan an sanyaka a qabarinka, wasu Mala'ikun 2 zasu zo maka! Sai nace dasu: Allah maku Albarka, ya saka maku da Alkhairi! To amma zan sake ganinku kuma? Sai sukace: A ranar Qiyaamah zamu tsayu gaba daya, wannan shine ranar halatta (domin dukkan mutane, Aljanu da mala'iku zasu halacce ta), sai naga sanda suka ambaci qiyamah sautinsu ya chanza, sannan sukace: Amma in ka kasance cikin yan Aljannah, zamu zamo tare ku zaka gammu.
Nace: to bayan naga Aljannah kuma naji sautin ababen cikinta, shin akwai sauran shakku agareni (na zan shiga ko za'a korani wuta)?
Sai sukace: Lamarin Shiga Aljannah lamarine da Allah kadai ya mallakeshi, kuma kai ka samu karramawa sabida ka mutu musulmi, abinda yayi saura shine a nuna maka ayyukanka (a qabarinka da qiyamah) da kuma mizani!
Sai fuska ta ta chanza har na kusa kuka, domin ina tuna zunubaina tamkar manyan duwatsu! Sai suka ce dani: Ka kyautata zatonka ga Ubangijinka, kuma ka qudurce cewa Ubangijinka bai zaluntar kowa, Sai sukai min sallama, sukai sama da sauri.....
Naga jikina akwance, sannan sai naji sautin kuka, sautine da na sanshi, Mahaifinane me qaunata da kuma dan-uwana, -subhaanallah, ina nakene yanzu?- sai na kalli jikina naga ana zuba masa ruwa, sai na gane cewar yanzu ana wanke gaawa ta ne! Sautin kukan nan na matuqar takuramin, amma duk sanda naji Mahaifina na cewa: "Allah ya sassauta maka, Allah maka rahmah" sai naji tamkar ana zubamin ruwan sanyi ne, sai suka rufe jikina da farin likafani.
Sai nace cikin raina: KAICONA ACE MA BAN TABA BARIN MINTI 1 BA A RAYUWATA FACE CIKIN AMBATON ALLAH, KO SALLAH, KO WATA IBADAH! Kaicona ace ina sadaqa dare da rana, kaicona kaicona!
Babban burina shine qabari, da abinda zai biyo bayansa, sai naji mai min wanka na cewa: shin zaku masa sallah ne bayan La'asar? Babana yace: Eh insha Allah -cikin kuka-! Suka dauki gaawata, ina kallonta amma bana iya magana ko motsi, suka shigar dani firij da ake sanya gaawarwaki, chan sai naji ana cewa: ku daukeshi ku kaishi masallaci! Suka daukeni inajin duk maganganunsu, babban abinda ya fi damuna shine kukan Mahaifina, kamar ince masa: kada ka damu yaa Baba, abinda ke wajen Allah yafi Alkhairi! Don Allah kabar kuka, domin ina shan radadi a dalilin kukanku, amma ko na fadi bazasu jini ba! Inajin sautukansu kuma ina gane muryar kowa, yan'uwana, kuma duk ina jin maganganunsu! Suka isa masallaci suka ajeni, sukai sallar la'asar, nai kwadayin dama ace ina taredasu muyi sallar nan nima nasamu lada! Chan bayan idar da sallah sai naji ladan na cewa: Jama'a kuzo muyiwa dan-uwanmu sallah!
Bayan liman ya soma sallah, sai ga Mala'iku 2 sun zo, daya na tambayar dayan adadin masu mani sallah, nawane cikinsu muwahiddai basu hada Allah da wani? Suna rubutawa! Bayan kabbara ta 3, wacce cikinta ake mani Addu'a, sai naga mala'iku na rubuta abubuwa masu yawa, sai nasan suna rubuta Addu'o'in jama'a ne! Nai fatan dama ace liman ya tsawaita wannan kabbara kada yayi ta 4, domin har na soma sararawa ina jin dadi! Sai yayi kabbara ta 4 yayi sallama! Suka daukeni suka kaini Qabarina............­.....


Mu hadu a na 6 don jin yanda zata kasance a Qabari.


**DUNIYAR MUTUWA**

(6)

Suka daukeni zuwa Qabarina, suna tafe cikin sauri, inajin Addu'ar da suke min, inajin Istirjaa'insu (shine fadin: Innaalillaahi wa innaa ilaihi raaji'un), ina jin kukansu da sukeyi, nikuwa ina cikin halin dimuwa da tsoron abinda zan taras, domin yanzu ina tuno zalunci da nayi, da kuma zunubaina, da kuma lokuta da na kwashe cikin shiririta da shirme maimakon Bautar Ubangijina, lallai yanayin akwai tsoro!
Bayanda suka isa qabarina, sai naji sautuka da maganganu masu yawa, inajin maganar masu sanyani a qabarina, inajin dayansu na cewa 'ku matso dashi, ku sakoshi ta nan, ku bude hanya........', yaa Allaah, abinda ake bani labari kuma nake gani munawa wasu, yau gashi gareni.
Suka shigar dani qabari, inajin wanda ya ciro gaawata na cewa 'Bismillaah wa alaa millahi Rasulullaah'!!
Aka soma shirya itatuwa, da kwaba qasa, ana sanyawa a qabarina, kamar nayi ihu nace: 'Kada kubarni anan don Allah, bansan me Allah ze min ba in kuka barni', amma ko na fadi bazasu ji ni ba! Naga duhu ya soma tsananta, sautin mutane na rarraguwa, amma ana jin qarar takalmansu da tafiyarsu! Inaji wasunsu suka tsayu a qabarina sunai mini Addu'a, Addu'arsu ta zamo debe kewa gareni kuma ta zamo sassauci ga qirjina, musamman daya daga cikinsu da naji yana cewa: "Ku roqa masa tabbatuwa domin yanzu ana tambayarsa".
Kwatsam sai qabarin ya soma matsewa, har naji tamkar za'a matse dukkan jikinane, na firgita har na kusa fasa ihu, sannan sai qabarin ya dawo yanda yake, chan sai malaa'iku 2 suka baiyana gareni, cikin sura me ban tsoro, jikkunansu masu girma ne baqaqe, idanuwan manya, idan suka qyafta ido tamkar walqiya, qumbunansu kamar zasu tabo qasa, a hannun dayansu akwai Guduma babba, wacce da ace za'a samu babban birni a buga masa ita, da dukkan birnin sai ya rushe! Dayansu yace min: Zauna. Sai na zauna.
Yace: Waye Ubangijinka? Shi kuwa me gudumarnan ya qwalo min ido.
Nace: Ubangijina shine Allah!
Nakasance ina amsawa cikin kidimewa, sai ya sake cemin: Waye Annabinka?
Nace: Muhammad s.a.w.
Yace: Meye Addininka?
Nace: Musulunci.
Sai suka cemin: Yanzu ka kubuta daga fitinar qabari.
Nace dasu: Kune Munkar da Nakiyr? Sukace: Eh! Da ace baka amsa ba da mun bugeka da wannan Gudumar, wanda sai kayi ihun da duk Halittu sai sunji ihunka in banda Mutane da Aljanu! Inda ace mutane da Aljanu zasuji ihun, da sai sun sume sabida tsabar ihunka! Kuma da sai ka nitse qasa tsawon zira'i 70! Nace: Godiya ta tabbata ga Allah da ya kubutar dani daga wannan, wanna falalar Allah ne shi kadai!
Sai suka wuce, bayan wucewarsu, sai na somajin wani zafi mai ban mamaki, jikina ya soma zufa yana karkarwa!!!!


Kubiyoni a rubutu na 7 don jin Abinda zai biyo baya!!!!


**DUNIYAR MUTUWA**

(7)

Bayan wucewarsu (Munkar da Nakir) sai na soma jin wani zafi a qabarina, jikina ya soma makyarkyata, naji tsoron kada ace qofar wuta aka bude sabida tsananin zafi, amma ba abinda nake ji illa tsananin zafi wanda ke fitowa daga jikina.
Chan sai wasu Malaa'iku 2 sukazo min, sukace: Assalaamu Alaikum warahmatullahi wabarakaatuhu.
Nace: Wa'alaikumus-salaam warahmatullahi wabarakaatuhu.
Sukace: Mu malaa'ikune, munzo nuna maka aikinka a qabarinka, da kuma tattara kyawawan ayyukanda ake maka kyautarsu daga nan Har rananr qiyaamah.
Nace dasu: wallahi tunda na mutu nake ganin ababen tsoro, ban zaci haka abin yake da tsanani ba! Amma zaku amincemin nai maku tambaya? Sukace Eh!
Nace: Shin ina cikin Yan-Aljannah? Bayan duk wannan abubuwa da nasha, shina akwai wani abu da zai iya sanyawa Allah ya saani a wuta?
Sai sukace: Kai Musulmi ne, abinda ya sameka, don kayi Imani da Allah da Manzonsa ne, amam shiga Aljannah ko wuta, ba wanda yasanshi sai Allah, sai dai munaso ka sa aranka cewa: Koda Allah ya sanyaka a wuta, to bazaka dauwama a cikinta ba, domin baka shirka kana kadaita Allah!
Sai na soma kuka nace: To idan Allah ya sanya ni a wuta, kwana nawa zanyi cikinta?
Sukace: ka kyautata zato ga Ubangijinka kawai, kuma ka sani, shi mai karamci ne!
Don haka yanzu zamu soma nuna maka ayyukanka, tun daga sanda ka Balaga har zuwa qarshen numfashinka a inda kukai hatsari!
Kuma zamu soma ne da Sallarka, domin itace bambancin Musulmi da Kafiri!
Amma ka sani, duk wani aiki na qwarai da kayi bazaka ga sakamakonsu ba, domin ayyukanka na qwarai dukkansu a sagale maka su!!!
Sai na ce cikin mamaaki: Me yasa?!! Kuma menene alaqar wannan da Zaafinda nake ji a jikina, wanda nakeji kamar an tattaro zazzabin duniya an taara min ajikina??
Sukace: wannan Nada Alaqa da abinda kakeji, sabida sakacinka wajen biyan baashinda ake binka na kudade da kaayayyaki! Kuma yanzu kana cikin hatsari babba!!!!
Nace cikin kuka: Ya za'ai kenan? Yanzu Baashi shine yasa aka Tsayar da Ayyukana, kuma nakejin wannan tsananin zaafin?
Sukace: Tabbas kuwa!!!


Yan-Uwa sai kuyi tunani ku gyaara kafin lokaci ya qure maku! Mu hadu a rubutu na 8 don jin ci gaban labarin!


**DUNIYAR MUTUWA**

(8)

Nace cikin kuka: Ya za'ai kenan? Yanzu Baashi shine yasa aka Tsayar da Ayyukana, kuma nakejin wannan tsananin zaafin?
Sukace: Tabbas kuwa!!!
Kwatsam maganata ta yanke, sanadiyar wani haske da ya bayyana gareni daga saman qabarina, haskenda ya shafe duhun qabarina ya haskakashi baki daya, wani irin qamshi mai dadi na fitowa daga cikinsa, ban taba jin daddaadan qamshi irinsa ba! Sai naji Hasken yace: Assalamu alaikum wr wb!
Na amsa masa: Wa'alaikumus-salaam wr wb, waye kai?
Yace: Nine Suratul Mulk (Tabaaraka), nazone don na nema maka rangwame wajen Ubangijinka, domin ka kiyayeni tsawon rayuwarka, kuma Annabinku Muhammad s.a.w ya baku labarin cewa: ina nemawa duk wanda ya kiyayeni kubuta a wajen Allah!
Nace: Maraba dake, surar da na haddace tun ina qarami, nake karantata cikin sallah da cikin gidana, gashi ayau ina matuqar buqatuwa gareki!
Tace: hakane, sabida hakanema nazonan, zanje in nema maka rangwame wajen Allah yanzu, duk wannan tsanani ya sameka ne a sabili da Baashi da ake binka wanda kai sakaci baka biyashi ba, kuma shine ya sanya aka qi nuna maka ayyukanka kuma kakejin zafi a jikinka!
Nace: to yanzu ya za'ayi na kubuta?
Tace: da dayan abubuwa 3 ne!
Nace cikin hanzari: Meye su?
Tace: Kafinda na fada maka wadannan hanyoyi, shin ko ka rubuta baashinda ake binka a takarda, domin magaadanka su biya maka?
Sanda naji wannan kalmar (Magaada) sai naji tsanani a raina, hawaye ya zubomin, domin na tuno dukkan iyaalai na, Mamata, Babana, Mataata, Yan'uwana da Yaarana! Kaicona, me ya samesu a baayana??? Sai na tuno Yarinyata qaramar sanda muke waya take cewa: "Tanaso na kawo mata Cocoa" to yanzu me zasu ce mata in ta tambaya ina nake? Ya rayuwarta zata daawo bayan mutuwata? Mataata me zatayi baayana? Yanzu ta zama #Bazawara kenan? Ya zatayi da wahalhalun Yaarana a bayana???? Nadinga tunane-tunane, hawaye nata zubomin, damuwata nata qaruwa!!!
Sai Tace dani: Kaman ka tuno wani abu ko?
Nace: Eh, Na tuno iyaalaina ne, ya zasu kasance baayana!
Tace: Sunada Allah, shi ya Haliccesu yake azurtasu, kuma shine zai jibinci lamuransu!
Sai wannan Magana ta zamo tamkar ruwan sanyi ga mai qishin-ruwa!!
Nai shiruuuu ina tunani!! Sai naji zafin jikina na qaaruwa! Sai nacewa Suratul-Mulk: Don Allah zan iya sanin baashin nawane ake bina?
Tace: Eh, na Tambayi Malaa'ikandake kula da ayyukanka, yace min Riyal 1700 ne: 1000 na abokinka ne da ake kira Abaa Hasan, 700 kuma guntu-guntun bashin mutane ne da kaci aka taara maka!
Nace cikin mamaki: Gutsa-tstsarin bashi?
Tace: Tabbas kuwa, domin kana sakaci da qananun baashi tun taasowanka, baka damuwa dasu balle ka biyaasu, to sune suka tarun maka!
Nace: To na su waye?
Tace: Riyal 5 na mai saida kayan abinci ne, ka sayi kayan abinci wajensa! Alokacin baka da kudi, ya maka magana kace zaka bashi...........haka­ dai tata lissafominsu........­.kudaden masu min wanki.......
Tace: Sabida yanda kuke Raina baashi, yasa da yawanku kukeshana wahala a qabarinku, Annabinku ashe bai gargadeku gameda baashi ba? Kuma ya gaya maku Shahidi dukda girman matsayinsa amma Baashi nasa a tsaida aikinsa?
Nace: Innaalillaahi wa innaa ilaihi raaji'un!! Yanzu menene mafita??? Wlh jikina zai tsints-tsinke sabida azaabar radadi!!!!!!!!



Mu hadu a rubutu na 9 don jin mafita! Sai mu kula mu biya baasussukandake kawunanmu tun da ranmu!


**DUNIYAR MUTUWA**

(9)
(Kada ku mance, Muna kan gabar da Suratul Mulk suke magana da wannan Mamaci ne gameda Mafita daga Uqubar da ya shiga a sanadiyar basussuka da ake binsa bai biyaba har ya mutu)


Suratul-Mulk tace min: Mafita dai dayan abu 3 ne kawai!
Nace menene su??
Tace: 1: Kodai wanda ke binka kudin nan ya yafe maka.
Nace: ai da yawansu ma sun mance suna bina bashi, wasuma basusan da mutuwata ba, wasu qila sun mance ni ma balle su yafemin, menen mafita na gaba?!
Tace: 2: Ko kuma magaadanka su biya maka bashin.
Nace: yaya magaadana zasusan da ana bina bashi ko halinda nake ciki yanzu? Ni gashi ban rubuta wata takarda dake dauke da haqqoqin (baashi) mutane baba balle su biyaamin, domin mutuwa ta zomin ne baa zato, ban shirya mata ba ban kuma kawota nan kusa ba!
Tace: To yanzu ya rage saura abu 1, zanyi maka qoqarinsa, wata qila yazama sanadiyar kubutarka, zan gaya maka shi idan na dawo insha Allah, amma yanzu na tafi!
Nace: Don Allah kar ki tafi, kada ki tafi domin inajin tsoro da firgici duriya bisa zafin jikina dake qaruwa.
Suratul Mulk tace: Bazan nesa da yawa ba, kuma zan tafine don neman mafitarka....
Sai ta tafi, na rage ni kadai cikin baaqunci da duhu, damuwa da baqin ciki sun tarun mini, sai na tuna wata addu'a:
"يا من لا يأنس بأنيس أبقاه, ولا يستوحش من شيئ أفناه, ويا أنيس كل غريب, ارحم في القبر غربتي, و يا ثان كل وحيد, آنس في القبر وحدتي"
(Ya Allah wanda baya debe kewa da wani abu don yaa barshi, ko yayi baqunci bisa wani abu da ya qaarar dashi, kuma ya ma'abocin duk wani baaqo, kajiqan baquncina a qabarina, ya na biyun dukkan guda -domin mutum shi 1 ne aqabari-, kadeben kewata cikin qabarina), sai na tuna ashe yanzu ba a duniya nake ba, na riga na wuce gidan aiki, nan ina gidan saka mako ne!
Ban aune ba sai naji sautin Mahaifina mai qaunata, yana cewa: Assalamu alaikum wr wb, (sai na amsa masa cikin tsumaye, amma kasshshshhh bazai ji amsawaata ba)! Naji yana cewa: Ya Allah ka yafe masa, Ya Allah ka haskaka mashigarsa (qabari), ka debe kewarsa!!! Sai najishi yana kuka yana cewa: Allah ka kaareshi, ya Allah ka shaida ni mai yarda ne agareshi, ya Allah ka yarda dashi!!! Sai ya wuce!
Sai naga Haske ya cika Qabarina bayan duhun-dake ciki sanda mahaifina ke mani addu'a, mala'ikunda ke ciki basu cemin komai ba har saida ya wuce, qabarina yaci-gaba da zamowa cikin haske, mala'ikun nan suka cemin: Addu'ar mahaifinka za'a dagata har sama madaukakiya, kuma da sannu Allah zai amsa masa, domin Addu'ar mahaifa karbabbiya ce!!
Kaico na, naso ace mahaifina bai daina Addu'arsa ba gareni, yanayin yanda naji dadinta a qabarina hatta a jikina!
Nacewa Mala'ikun: in tambayeku wani abu?
Sukace: Eh!
Nace: Tun yaushe na rasu? Kuma yanzu qarfe nawa ne?
Sukace: Kwananka 3 da rasuwa yanzu, yanzu kuma lokacin sallar azahar ne!
Nayi mamakin gudun lokaci, yanzu duk wadannan abubuwa a tsawon kwanaki 3 akai kachal??? Yanzu duk wannan tsananin duhu da nake gani kafin haskenda ya haska qabarina a dalilin Addu'ar mahaifina, yanzu duk lokacin Azahar ne?
Malaa'ikun sukace: Tafiyar dake gabanka mai tsayi ce, fatanmu Allah ya taimakeka!
Na soma kuka mai tsanani wanda ban taba irinsa ba a rayuwata, nace cikin raina: *Tsarki ya Tabbata ga Allah!!!! Sau nawa na zamo mai mantuwa gameda wannan Haali???*


Mu hadu a rubutu na gaba!!!


**DUNIYAR MUTUWA**

(10)

Nace: sau nawa na kansace cikin shagala gameda wannan hali da zan shiga a qabarina!!!!!
Sai mala'ikan yace: Qabarinka zai ci gaba da zamowa cikin haske tsayin kwanakinda Allah Yaso albarkacin Addu'ar mahaifinka!
Ziyaarar mahaifina sai ta zamemin debe kewa, nai kwadayin daama dukkan makusantana su dinga ziyartata, daama dukkan abokaina su dinga ziyartar Qabarina!!
Nayi kwadayin daama ace mahaifina zaiji maganata a qabarina, da sai ince masa: Yaa Baabana inaso ka biya min baashi da ake bi na, inason kai min sadaqa, inason kai min addu'a......
Saidai babu yanda za ai yaji ni, na tuna fadin Allah (........kuma akai shaamaki tsakaninsu da abinda suke kwadayi)!
Naji zafin jikina kamar yana sauka, saidai wani lokacin yakan qaaru, sai nai zaton hakan nada dangantaka da ziyarar mahaifina, ashe wani abune chan daban!
Ban dauki lokaci ba sai wani haske ya baiyana gareni, na gane hasken da ganinsa, hasken Suratul Mulk ce!
Tace: Nazo maka da bushaara 2!
Nace cikin sauri: Menene su??
Tace: Na farko: Wannan mutumi dake binka Riyaal 1000, ya tuno kuma yace ya yafe maka!
Nace: Alhmdlh, wannan qila shine dalilinda yasa naji sauqi-sauqi kenan!
To menene bushaara ta 2?
Tace: Na nema maka afuwa wajen Allah, amma abin yaci tura, don ba'a yafe haqqin yan adam, amma Allah ya turo malaa'ika wanda aka wakilta wa mafarki, zaije wajen daya daga cikin yan'uwanka yai masu nuni da halinda kake ciki, wata qila su gane sai su biyaa maka!
Nai mamakin wannan magana sosai!
Sai tace min: wurin wa kakeso yaje cikin makusantanka?
Na tuno Mahaifiyata, sai na tuna idan ta ganni a mafarki zatai ta kuka ne kawai bazata baawa mafarkin muhimmanci ba balle ma ta fassaraashi ba!!!! Nata tuno mutane, sai na tuno mafi kusancin mutane gareni bayaga mahaifina, itace Mataata wacce ta qware wurin fassara mafarki, Mataata kenan mai sona mai cikan Alqawari!!! Sai nace: Inaso a nunwa mataata wannan mafarkin!
Sai Tace: zan fadawa malaa'ikan, kuma in roqa maka Allah ya gaggauta kubututarka ya share damuwarka!
Ta tafi, qabarina yaci gaba da zamowa cikin hasken Addu'ar mahaifina, na zauna ina jira tamkar wanda ke tsare a purzina, lokuta na wucewa amma ban sanin dare ko rana, face wasu lokutan nakanji sautuka, wasu lokutan nakanji sautin taakalma na masu wucewa, da haka nake gane cewa an kawo sabuwar gaawa kusa dani, nakanji wani zubin mutane na dariya, sai nake mamakin ace mutum na dariya bayan mu gashi muna qasansu a tsare!
Na dauki lokaci mai tsawo, sai naji zaafin jikina na qaaruwa, sabida tsaabar zaafi har nakusa rusa ihu, jiyna nake tamkar ina cikin tandar waina, sai tsorona ya qaru!
Chan kuma sai naji zafin na raguwa kadan kadan, har naji ta sakeni gabaa daya, sai naji tamkar na fito shan iska ne sabida dadi! Na rikice sabida murna bansan me ya faru ba! Na soma mamakin sabon yanayinda nake ciki yanzu, menene ya faru????


Sai mu hadu a rubutu na gaba don jin abinda ya faru!!!


**DUNIYAR MUTUWA**

(11)

Ina cikin Murna da mamakin saurin sauyinda na samu, na yanayin da nake ciki, na rasa dalili, kwatsam sai naga Haske ya baiyana gareni, Hasken Suratul Mulk ne!
Tace dani: Bushaararka da abinda zai sanyaka farin ciki!!
Nace: Madallah da ke, koda yaushe da Alheri kike zuwa, menene ya faru?
Tace: Malaa'ikan Mafarki ne yaje wajen Matarka cikin barcinta, ya nuna mata gakanan akan tsaani cikin damuwa da qunci, ya rage saura matakala 7 ka haye, amma ka kasa hayewa!
Sai matarka ta farka kafin sallar Asubah, ta tuno mafarkin ta tuno ka, sai tayi kuka ta maka Addu'a, baayan ta idar da sallah, sai ta dauki littafan Fassarar mafarki, taga maganganu dai masu yawa kan fassarar irin mafarkin nan, bata cimma matsaya ba, amma dai ta san cewa koma menene, kana cikin Baqin ciki!
Da safiya tayi sai ta kira wata maata awaya, wacce ta shahara wajen iya fassara Mafarki, sanda Maatar ka ta tambayeta gameda mafarkinta, sai tace: Yaake Yarinyata, Mijinki ana binsa baashi, kuma yanzu haka yana tsare a Qabarinsa, kuma Baashin Riyal 700 ne ko kuma 7000, Allah dai shine mafi sani!
Matarka tace: to yanzu ya zamuyi mu biya masa?
Maatar tace: Allah ne mafi sani, ki Tambayi Malamai!
Bayan nan sai Maatarka ta kira daya daga cikin maatayen Malamai, tace: Don Allah ki Tambayan min Malam: Ya zanyi idan mijina ya rasu, kuma ana binsa baashi amma bamusan wanda ke binsa ba, ya zamuyi mu biya?
Matar Malamin ta Tambayeshi sai yace: Kuyi sadaqa da kudin, Muna Faata Allah ya warware masa Bashinsa dashi!
Maatarka tanada wani Zinari, wanda yakai darajar Riyal 4000, sai ta tafi wajen Mahaifinka ta bashi labari, sai yaqi karban Zinarin, yace zai biya kudin duka a aljihunsa, Maatarka ta Rantse da Allah sai yaa Amsa, tace: ai wannan cikin dukiyar Mijinane, kuma daama ina faatan masa wani abu baayan Mutuwarsa, kuma ina faata kada Allah ya Haramta min shi a Aljannah!
Da Mahaifinka yaga yanda ta naace, sai ya amshi zinarin aka sayar, yaa cike kudin ya zama Riyal 10000, sai ya bada su duka sadaka ga wasu miskinai, shine Allah ya yaye quncinka da damuwarka, nikuma nazo don qara kwantar da Hankalinka!
Nace: Alhamdulillaah! Yanzu banjin kowane radadi a jikina, ji nake kaman ina qulle sai aka kwance ni, lallai wannan falalar Allah ce, dakuma qoqarinki wajen taimakamin wurin sauke Baashi na!
Sai Tace min: Godiya ga Allah da ya tafiyar maka da Damuwarka da baqin cikin ka! Don haka yanzu Malaa'iku zasu zo domin Bijiro maka da Ayyukanka...........­.



"Yan'uwa munga illar baashi, munga halinda wannan mutumi ya shiga, kuma tabbas haka zata faru ga duk wanda ya mutu da baashi a wuyarsa! Ba komai ya ja masa haka ba illa tsawaita mutuwa, ita kuwa zuwa take KWATSAM!
Ka/kiyi qoqari ka daina cin baashi, idan kuma kaaci, to ka rubuta a littafi ka ajiye, don da zaarar ka/kin mutu, a tsanake za'a dauko a biya maka, kuma idan so samu ne, duk sanda mutum ya Mutu, kafin a bizne shi, MAKUSANTANSA SU SOMA BINCIKA KO ANA BINSA BAASHI, Domin sauwaqe masa"


Allah ya sauqaqa mana.


**DUNIYAR MUTUWA**

(12)

Suratul Mulk Tace mini: Godiya ga Allah da ya tafiyar maka da baqin ciki! Yanzu malaa'iku zasu zo domin bijiro maka da ayyukanka da kayi a duniya!
Nace: to bayan wannan akwai wani hatsari a gabana?
Tace: Hanyar gaskiya tanada tsayi, wata qila ya daukeka shekaru masu yawa, sai kayi shiri!
Nace: Shekaru kuma?
Tace: Dayawa daga wadanda ke kwance a Qabari #Anai_masu_azaabane_­bisa_laifukanda_suke­_rainawa, a wurin kuma wadannan laifuka Masu girma ne!
Nace: Misalin me kenan?
Tace: mutane dayawa anai masu azaba sabida rashin Tsarki baayan Fitsaari, sai ya tafi sallah amma yana dauke da najasa, ya tsayu gaban Allah alhali najasa na jikinsa ko tufarsa!
Nace: masu wannan Sunada yawa ne?
Tace: Mafi yawan wadanda akewa azaaba a qabari #Dalilin_wannan_ne!
Baya ga wannan, akwai wasu abubuwa da ake azabtar da mutane masu yawa dasu a Qabari, irinsu #Annamimanci, #Cin_Dukiyar Marayu, #Saata, #Ribaa d.s!
Akwai kuma wadanda akewa Azaaba a qabarinsu don tsarkakesu kafin Tashin qiyaamah, sun huta da Azabar Jahannama kenan, domin tafi tsanani da azaabah, hakanan akwai wadanda a qabari sushaa Azaaba kuma a Qiyaamah su shiga Jahannama!
Nace: Yaya zan kubuta daga Uquwbar Allah kuma meye mafita?
Tace: Ayyukanka dai a yanzu sun Yanke sabida mutuwarka, abubuwa 3 ne kawai suka rage maka, sune: 1: Addu'ar Yaranka, Iyayenka da Yan'uwanka gareka!
2: Sadaqa mai gudana, wacce zata ci gaba da gudana har bayan Mutuwarka!
Nace: aikuwa na tuna wani abokina da muke taara kudi wajensa don gina masallaci a wani qauye!
Tace: Wataqiyla Allah ya ninka maka laadanka, domin Allah yafi ninka laadan wanda ya gina masa daki!
Nace: Menene abu na 3?
Tace: Shin kaa taba yaada ilimi? Ko kuma sanar da wani wanda bai sani ba dokokin Musulunci?
Nace: a'a, chan sai na tuno kudade da muka shaa hadawa don buga littafai na Addini cikin yaruka daban daban muna rabawa kyauta! Nace: kaicona, ashe ga abubuwa masu lagwada dayawa na barsu ban yawaita su ba! Naji tamkar na tsandara ihu ine YAKU WADANDA KUKE RAYE, KU TSERATAR DA KAWUNANKU! Kuma kuyi guziri na abinda zaku taras bayan mutuwarku, wallahi da ace kunga abinda na gani, da bazaku taba fitowa daga Masallaci ba, da kun ciyar da dukkan dukiyoyinku!
Nacewa Suratul Mulk: To Yanzu Ayyukana na qwarai za'a ninka min su? Kuma wasu ayyukan na qwarai zasu dinga zuwa min?
Tace: Mamata dayawa ayyuka na qwarai na zuwa masu dayawa a farko-farkon mutuwarsu, sananan daga baya su dinga ragewa, abisa mancesu da Yan'uwansu zasuyi su dena masu Addu'a!
Nace: Ashe Yan'uwana, Yaarana da abokaina zasu mance ni bayan mutuwata? Nace gaskiya zai wahala su manceni haka sakai!
Tace: to shikenan, zaka gani, hatta ziyaararsu ga qabarinka zata rage, bayan watanni da shekaru, sai kaga babu wanda zaizo ya ziyarceka balle ya maka Addu'a!!!!!!


Mu hadu a Rubutu na gaba!


**DUNIYAR MUTUWA**

(13)

Tace: to shikenan, zaka gani, hatta ziyaararsu (Yan'uwanka/abokai) ga qabarinka zata rage, bayan watanni da shekaru, sai kaga babu wanda zaizo ya ziyarceka balle ya maka Addu'a!!!!!!
Nayi kuka kuka mai tsanani, don na tuna kakana sanda ya rasu, muna zuwa qabarinsa duk kwana 7, muka dawo duk wata daya, har muka mance shi, na tuno sanda nake raye yanda nake mance mamata wadanda muke tare, yau nima gashi na bi sahunsu!
Tace dani: #Mai_hankali_shine_w­anda_Yayi_Aiki_don_m­utuwarsa da makomarsa! Sai dai zan fada maka wani abu!
Nace: menene shi?
Tace: Akwai wanda zai dinga maka Addu'a kuma ba cikin iyaalanka yake, kuma yana naima maka Gaafara, al-hali bai sanka ba!
Nace: yaya haka?
Tace: Dazunnan wani mutumin qwarai a India ya Maka Addu'a yace: Allah ka gaafartawa Muminai Maza da Mata, da Musulmai Maza da Maata, raayayyunsu da Matattunsu, sai Allah ya rubuta masa Kyakykyawan Aiki gwargwadon rayayyu da matattu, sai Allah cikin falalarsa ya baka Kyakykyawan aiki cikin Addu'arsa!
Hakanan akwai wani Mutum daga Turkiyya (Turkey) ya gina Masallaci a sadaqa, sannan yace: Ya Allah ka sanya laadanshi ga Al-Ummar Annabi Muhammad s.a.w, rayayyunsu da Matattunsu!
Hakanan akwai wata Mata Tsohuwa da Masar, ta yanka Akuya tai sadaqa da ita, sannan tai sadaqa da Ladanta ga Mamatan Musulmai.
Sannan Akwai wani Saalihin Mutum daga Magrib (Moroco) yayi Umara, sannan Yayi Addu'a ga dukkan Musulmi asada yake tawaafi, dukkan irin wadannan da ire irensu laadansu da Addu'o'insu na riskarka! Kai Hatta Malaa'iku na maka istigfaari!
Sanda naji wadannan maganganu da busharori, sai nai Farinciki dashi, wanda ban taba irinsa ba!
Bayan hakane ta cemin zata tafi!
Sai baqunci ya kaamani sabida wucewarta, amma sai nakejin nishaadi a jikina,zuciyata a yalwace! Wani zubin kuma qirjina sai ya quntata kamar an daura duwatsun duniya akaina!
Babu wanda ya fadamin, amma na gane dalilin yalwatar qirjina shine: Addu'o'in Musulmai dake isowa gareni daga kowane lungu da saqo na duniya! Quncin nan kuwa quncine na qabari wanda bayada makawa kuma baya misaltuwa!
Haka kwanaki suka dunga wucewa, babu mai deben kewa bayaga ga Addu'o'indake iso min! Ko ziyaarar Mahaifina, Yan'uwana da Abokaina, wanda ita ahankali ta dinga ragewa, har takai ba mai ziyartata saidai Addu'o'I suma jefi-jefi! Haka komai ya yanke!
Kawai Addu'ar #Mahaifiyatace bai yanke mini ba, musamman a kaso 3 na qarshen dare, haqiqa Addu'arta ta fi debemin kewa akan kowa!
Haka dai duk wasu Ayyuka da Addu'o'I dake isomin suka dinga yankewa, naga lallai nashiga mataki mai hatsarin gaske, domin ina cikin damuwa matuqa duba ga MIZAANI da zan tsayu ran qiyaamah! Da. Yanda Za'ai MINI HISAABI bisa duk qarami da babban aikina!
Ya Allah Adfuwarka nake nema, Ya Allah rahamarka nake faata, Ya Allah jin qanka nake kwadayi!
Sai dai kash........ Addu'ata bazata amfaneni ba ayau, don mahallinta ya riga ya wuce!!!!!


Mu hadu a rubutu na gaba.


**DUNIYAR MUTUWA**

(14)

A haka dai kwanaki keta shudewa ina kwance a qabarina, wani zubin nayita kuka, amma da zaarar na tuno faadin rahmar Allah, sai na samu sauqi!
Suratul Mulk dake zuwamin itama ta dena, na rasa dalili, a qabarina duhune mai tsanani, baana iya tantance dare daga raana!
Na tuno wasu Zunubai da Laifuka da na aikata a lokacin rayuwata, naga taarin zunubaina tamkar Manyan duwatsu ne, amma shin Allah zai gaafartamin su kuwa?
Da yawa nakan zargi kaina bisa laifukannan, ina nadama bisa kwanakin rayuwata da suka shude cikin shagala da rafkanwa!
Ashe Allah bai min tsaiko ba? Ashe bai rufamin asiri ba? Ashe bai yalwata min ba? Ashe bai Azurtani ba? Zunubai nawa na sani amma dukda haka nai tsaurin kai na aikata su?
Salloli nawa ne na jinkirtasu banyisu akan lokaci ba? Sallolin Asubahi nawa ne na makara nai bacci ban yisu a Jam'I ba? Ayyukan Alkhairi nawane na qi yinsu na tsaya ina jan lokaci akansu banyi su ba?

Sanda na tuna dukkan wadannan, sai nai kuka kuka mai tsanani, bansan tsawon kwanakinda nai ina kuka ba, domin bansan lokaci ba, dare da rana duk dayane a wajena, idan da zance nayi kukan wata 1, da bazance na kai tsayin lokacin ba!
Ana cikin hakane, wani haske mai qarfi ya hasko a qabarina, Tamkar raana ce ta sauko cikin qabarina, sai naji Malaa'iku na taya junansu murna suna cewa: Bushaararku da Rahma.... Na tsinci kaina tsakanin Maaki da Murna gamida neman sanin meke faruwa???
Chan kuma sai na sake ganin wani hasken kuma ya sake Haskowa wanda ya maamaye qabari na, chan sai naga wani Malaa'ika yazo yacemin: Albishirinka ya kai Mumini da saukar Rahmah!
Nace: Jazaakallahu Khairan! Amma me ya faru?
Yace: Haqiqa abinda ya faru shine watan Ramadan ya tsaya, kuma watane da ake gafara da Rahma gamida Yantarwa daga wuta a cikinsa, kuma cikinsane malaa'ikundake qasa suke haduwa da wadanda ke sama, kuma cikinsane daya daga cikinku ke kubutu a bisa Addu'o'in Musulmai, kuma ma'aunin kyawawan Ayyukanku ke qara nauyi!
Nace: Wa yakai Girman Allah, wa yakai girman Lamarinsa, wa yakai girman karamcinsa????? Daama (iko) nawa yake ba rayayyu da matattu?
Mala'ikan yace: Allah baaya son sanya kowa a wuta, kuma baaya son azabtar daku, saidai kun cika sakaci da yawa, da kuma raina qananun zunubai, da kuma yanda kuke bijire masa bisa ni'imominsa gareku, wadannan sune sukafi Halakar daku!
Yanzu musulmai sun soma Sallah, ga Malaa'iku nan suna daukansu, kuma suna daukaka Addu'o'insu ga Allah, wata qila kuwma ku samu tausayaawar Allah!
Sai ya wuce!
Haka dai haske ya ci gaba da mamaye qabarina, ina jin sautin sallar mutane, inajin Addu'o'insu, ni kuwa ina kwance a qabarina ina cewa Amin, Amin, Amin ina kuka!!! Na samu natsuwa, Hankalina ya kwanta, na zamo cikin Farin ciki!!!!!!


Mu hadu a rubutu na gaba!


**DUNIYAR MUTUWA**

(15)

Haka dai Kwanaki sukai ta gudana a gareni cikin Ramadan, koda yaushe Haske na sabuwantuwa a qabarina, chan kuma sai naji wani qamshi mai dadi tamkar qamshin Almiski wanda nake shaaqa a duniya, amma wannan yafi qarfi, chan kuma daga nesa wani mutum ya baiyana gareni, naga kamar yana tahowa gareni ne!
Nayi matuqar mamaki, a karon farko da naga Halitta cikin qabarina a surar dan-Adam! Yana ta tahowa wajena nikuwa na dimauce, da ya iso, sai naga fuska kyakykyawa sanye yake da tufafi masu tsananin haske, sai na gane lallai wancan qamshin Al-miski da nake ji daga jikinsa ne, yace min: Assalamu Alaikum wr wb!
Na amsa masa: Wa'alaikumus-salaamu­ wr wb, na kalleshi cikin mamaaki, kamar in tambayeshi "waye kai?"!!!!
Yaga alamun mamaki a fuskata sai yayi murmushi yace: Nazo makane don sanar dakai Rahmar Allah gareka da kuma Gaafara bisa zunubanka!!!
Nace: Kaima Allah ya maka bushara da abinda zai faranta maka rai, waye kai? Kuma ya kasan haka? Domin wannan shine karon farko da naga mutum cikin Bani-Aadam a qabari na!
Yace: Ni Ba dan Adam bane!
Nace: to kenan kai Malaa'ika ne cikin surar Yan-Adam?
Yace: a'a, ni ba Malaa'ika bane kuma!!!
Nace cikin mamaki: to waye kai kenan? Wallahi ka rikitar da qwaqwalwata, tsakanin farin cikin ganinka/zuwanka da kuma tsoron kai waye!
Yace: wata qila bazaka tuna ni ba, sai dai Allah ya saamar da nine daga ayyukanka na qwarai, Sallarka, Azuminka, Hajjinka, Sadaqarka, Addu'arka, biyayyarka/­kyautatawarka ga iyayenka, shine Allah ya sanyani inyi wannan sifa don yi maka bushaarah da gaafarah!!!!
-Yaa Allah, gareka godiya take har sai ka yarda- na fadeta sabida murna da farinciki ban sani ba-
Sannan nace: To me ya hanaka zuwa gareni sanda na mutu, me yasa ka makara bakazo ba har tsawon wannan lokaci??
Yace: Baashinda kaci shine ya tsayar dani da kuma zunubanka, wadanda sune suka hanani zuwaana gareka, amma baayanda Rahmar Allah ta sauka gareka kuma Allah ya Lullubeka da Gaafararsa shine Allah ya min izinin zuwa a wannan lokaci.
Nace: to wannan na nufin zan zamo cikin Yan Aljannah, kuma Allah bazai mini Azaabah ba?
Yace: wannan Saninsa na ga Allah, ba wanda ya sanshi baayansa, domin yanzu gabanka akwai Hisaabi da Miyzaani (Ma'aunin ayyuka) a ranar qiyaamah, wanda shine zai nuna maka makomarka, ananne za'a auna haqqoqin mutane da kuma sauran abubuwanda bazasu baiyana ba gareka sai ranar qiyaamah!
Nace: Misalin me kenan?
Yace: Da yawa daga mutane suna zaluntar junansu, sannan wanda aka zalunta zaice bai yafe maka ba! To anan ne za'a tsaida su gaban Allah, ayi masu hukunci!
Sai maganarsa ta bani tsoro!
Yace: Kuma lallai abinda ka aikata a qarshen rayuwarka ya amfaneka!
Nace: menene shi?
Yace: Da ace zaka tuna, lokacinda kuka hatsari kalmarka ta qarshe itace ASH-HADU AL-LAA'ILAAHA ILLALLAAH WA ASH-HADU ANNA MUHAMMADAR-RASULULLA­AH! Yace ba qaramin Farin Ciki Malaa'ikun Rahmah sukai ba da ka fadi wannan kalmah! Domin kaa cika da kalmar Tauhidi! Kuma kaa tabbata akan Musulunci a lokacinda shedan ke qoqarin kawar dakai daga Tafarkin Musulunci zuwa Nasaaranci ko Yahudanci, a lokacin Malaa'ikuna daama da hagunka suna shirin daukan ranka, na daama sune masu daukan Raayukan Musulmai, na Hagu kuma masu daukan Rayuwar Kafirai, sanda ka fadi Kalmar shahaadah, sai Malaa'ikunda ke daukan Rayukan Kafirai suka tafi, masu daukan Musulmai sune suka tsaya suka dauki Ranka!


Mu hadu a rubutu na gaba! Ya Allah ka tabbatar damu a lokacin mutuwa, ka bamu ikon cikawa da kalmar shahaadah!


**DUNIYAR MUTUWA**

(16)

Nace: to shin akwai wani abu da yayi min amfani bayaga Kalmar shahaadah?
Yace: Eh akwai, Nasiharka ga Matuqin Motar nan akan ya dena shan sigaari, dalilin hakane Allah yasanya kakejin Qamshin Miski a qabarinka. Hakanan Kiran mahaifiyarka da kayi a waya, duk kalmah 1 da ka furta mata ana rubuta maka Laada 1 da ita!
Hakanan kiran Matarka da kayi da sanya Yaarinyarka Farin ciki da kayi sanda kuke waya! Amma saidai bisa babban munanawarka ga Yaarinyarka, an rubuta maka Zunubi 1 babba!!
Nace Cikin tsananin Mamaki: Yaya kuma munanawata ga Yarinyata???
Yace: #Kaace_mata_zaka_daw­o_bayan_lokaci_qanqa­ni (bakace insha Allah ba), kaga anan kayi qarya tunda baka dawo ba Ajalinka ya cika, hakan yasa aka rubuta maka zunubi 1 na qarya, inda ace ka tuba kafin mutuwarka da ka more!
Nayi kuka nace: Wallahi ni ban nufin qarya ba gareta, ni nayi nufin haqurar da ita bisa nesa da nayi!
Yace: ai koma menene, kamata yayi ka fadi gaskiya, domin Allah nason masu gaskiya, kuma yana qin qarya da maqaryata, ku Matsalarku itace kuna sakaci dayawa!
Sannan yace: Hatta muguwar Addu'a da kayiwa ma'aikacin jirgin saman nan an rubuta maka zunubi da ita, domin ka Munanawa musulmi bisa abinda babu ruwansa cikin abinda ya sameka (na rasa tikitin jirgi)!
Nace: Wayyo Allah, duk manya da qananun laifukana an rubucesu!
Sai ya dawo yana cewa -tamkardai yanason rarrashiyna- me yakai kyawun aikin hajjinka akai-akai!! Itace mafi girman abinda ya daga matsayinka wajen Allah, hakanan Umrah da kakeyi akai-akai!
Nace: -ina mai son jin hankalina ya kwanta- domin ya sanyani na firgita ga lamarin ma'auni ran qiyaamah: Wani aiki ne mafi girma wajen Allah da aka rubuta min?
Yace: cikin falalar Allah gareku, koda kun aikata aiki me kyau guda 1, to ana ninka maku ita 10 ne, har zuwa 700 har zuwa ninkin baninki! Mafi falalr ayyukanka kuwa sune ayyukanda Allah yafi so #Farillai!
Nace: Salloli 5?
Yace: tana cikinsu, amma harda Azumin Ramadan, Zakkah, Hajji, wannan sune mafi soyuwan Abu da baawa zai kusanci Allah da su! Kuma Farillai (Waajibai) sunfi soyuwa ga Allah fiyeda Nafiloli!
Kuma yanzu zan gaya maka wani abu da kayi wanda Allah ya rubuta maka babban laada baaya ga Farillai!!
Nace cikin Shauqi: Menene shi?
Yace: zaka iya tuna wata rana kana Umrah cikin ramadan, sanda kana dan shekara 20, lokacin ka fito daga Masallaci mai Alfarma, kaga wani mutum na sayar da kaayan buda baaki ga masu Azumi, sai ka sayi na Riyal 100 ka rabas kyauta?
Nace: Eh, na tuna, kamar jiya akai, amma wannan yafi umarah ta girma?
Yace: zan tuna maka wata mata tsohuwa da ka ganta baata iya chakuduwa da mutane wajen karban sadaqar da kake rabaswa, sai kaje wajenta ka bata dauri 2????
Nace: Eh, haqiqa na tausaya mata ne ganin rauninta da shekarunta!
Yace: To wannan Maata daga Yamen take, Duk Addu'ar da tayiwa Allah, Allah baaya mayar mata, sai ya karba mata, tana cikin mafi nagartan Baayi, kuma ma'abociyar tsayuwar dare ce, wallahi da zatai Rantsuwa ga Allah, Allah sai ya cika mata rantsuwarta!
To tayita maka Addu'a, hakanan har lokacinda take shan ruwa, haka taci gaba da maka Addu'a har yamma, ita faqiriya ce ba wanda ya damu da ita, tareda ita akwai malaa'iku dake kai Addu'o'inta ga Allah, bisa Addu'o'inta da kyautatawarka gareta, aka rubuta maka Laada me girma!
Aka hada maka Laadan Umararka, Raba kyauta ga masu shan ruwa (wadanda sukai azumi) da kuma Kyautatawarka ga Tsohuwarnan, dukda laadan wannan tsohuwa da ka samu nan take aka dagashi sammai.




TAMBAY: Dan-Uwa: shin ka duba abubuwanda aka fadi a wannan qissar: nawa kakeyi? Shin ka auna kanka da Tsohuwarnan, ya abin yake?
A kullum ana baaka qissar nagartattun Mutane ne don kayi koyi dasu, bawai don ka karanta kaji dadi ba!



*Koma Saman Shafi*

→Labarai
1234...9899100»

Share|

Kaima shiga a tattauna da kai
* No boards.

Online: Guests: 1


→Ra'ayin jama'a game damu

 IDAN KANA BUKATAR A TALLATA MAKA HAJAR KA A WANNAN SHAFIN DA SAURAN SHAFUKAN MU KANA IYA TUNTUBAR MU TA WADANNAN HANYOYIN KAMAR HAKA:


Email: bjournalist55@hotmail.com

Phone No: 09035830253

Facebook: Basheer Journalist Sharfadi

Address: Ittihad Computer Centre,  No 92 Daneji Kano


MAI TALLA SHI KE DA RIBA


*Bayanan ka*
Browser din da ka hawo Mozilla

Kasar da kake United States

Adadin Maziyarta 273689

Adadin Wadanda Sukayi Comment 65691

A Wadanda Suka Shiga Tattaunawar Mu 54


Follow @bjournalist55
→Yi Adding Dina Ta Facebook
→Yi Like Na Dakarun Sunnah Page
→Yi Like Dina Ta Facebook

*Shafuka Masu Alaka Da Mu*

→Basheer Sharfadi wordpress
Basheer Sharfadi Blog Spot
UP
→Home

Basheer Journalist Sharfadi (Abu Hafsah)
ISLAMIC DATE
  • phpimg2.php?it&ic=yellow



  • Click to Sms
    Click to Call


    Basheer journalist sharfadi3
    Coollogo com-1281358

    Teya Salat